Tuesday, 13 November 2012

A BRIEF HISTORY OF CRCN LCC, DONGA


ZUWAN MISSIONARI  A GARIN DONGA DA
                                AYYUKANSU
Gabatarwa
  Zaku Zama shaiduna a Urushalima da duk kasar Yahudiya, da ta Samariya,har ya zuwa iyakar Duniya”, (AM. 1:8b).Wannan aya ta zama gaskiya cike da iko kuma, bisa kan mabiyan Almasihu. Yesu Almasihu ya bada wata doka kuma cikin Matta 28:19, yana cewa , Ku tafi cikin Duniya  duka, ku yi bishara ga dukan halitai”.
Masu bi na farko basu iya gane da wannan sossai ba , sai ran Pentecost tukunna, lochachinda Ruhu mai Tsarki ya zo bisansu. Daga wannan ran ace ekklisiys ta kafu ta wurin shelar Bishara wadda su suka yi.
Kafuwar iklisiya a Urushelima ran Pentecost, bata tsaya wuri daya ba, amma ta ci gaba da yaduwa har zuwa nan Nigeria.Turawa daga yammancin duniya suka dauki nauyin kawo Bishara nan kasarmu ta bakar fata. Ba Africa kadai ba, amma har cikin garin Donga.
FARKON FARAWA
   A cikin shekara ta 1902 wani Likita mutumin kasar Jamus, mai suna Likita (Dr) Karl Kumn ya kafa wata kungiya ta yadda bishara a kasar Inglila ya rada wa kungiyar da fari suna “Sudan Pioneer Mission”, (SPM). A 1904 an canja zuwa “Sudan United Mission”, (SUM). Ya zaga yawancin kasashe na Yammacin duniya, yana baza labarin wannan Kungiya da manufarta. Shi Likita Dr. Kumn ne da ya zama Shugaban wannan Kungiya. Duk mutanen dake cikin wannan kungiyar da su hudu (4) ne, wato Dr. A. Bateman, Mr. G. Burt, da Mr. Lowry Maxwell (Langalanga).
                Da isowarsu nan Nigera, Gwannatin Mallaka wadda Headquater take “Zungeri”can Niger State, ta umurcesu, su wuce zuwa can Wase, Plateau State su kuma kafa tungarsu a bishara a wurin. Amma abin tausayi shine, shekara daya kawai suka yi a wurin, tungar su ta ci wuta.Wato a cikin 1905 kenan.Wannan ya tillassasu kaura daga can Wase zuwa wani wuri karbabiya agaresu. Saboda haka a cikin shekara ta 1906, suka zo Ibi da Wukari. Nan ne suka kafa sabobin tungogin Bishara.Wadanda suka zo Wukari sune:
                Mr. J.L. Maxwell da John Young su suka bude gidan Mission na farko a wukari a cikin 1906. A lokaci guda kuma, cikin shekarar, Likita Dr. Kumn ya koma can Ingila domin nemo karin Mishinari domin wa’azi. Har yanzu cikin shekara ta 1906 din ne reshen “Sudan United Mission” ,(SUM) ta kafu a kasar America.
GARIN DONGA
                Kafin Mission su zo nan yankin Wukari Federation, ana kiran Wukari “Oka”, Takum kuma “ Kapatikari”, saanan kuma Donga kuma ana kiranta da suna “Kacho” (Big Wall).A cikin 1907, Mr. Guinter Hoover, Mr. Der, da shi Mr. J.L Maxwell Suka zo Donga, a zamanin  Gara Sonyonga Garbosa I ya nuna masu fili suka kafa bukarsu a wurin. Daga nan ne suka shiga cikin kasuwa suka fara shellar Bishara ta farko, a nan Donga cikin shekara ta 1907.     Bayan yan kwanaki suka koma wukari da Ibi inda suke da zama. Suna zuwa loto – loto domin yin Bishara. Da bukata ta taso da a sami mutum da zai yi zama a Donga domin yin Bishara na din din ta tsananta, sai aka aika zuwa Ingila, domin biyan wannan bukata, Mallam Whiteman suka zo Nigeria a 1910 da matarsa, suka zauna a Ibi na tsawon shekara daya suna koyon Hausa.Da suka gane da harshen Hausa, sai suka zo nan Donga a Janairu 1911.Suka Gina gidansu na zobe guda daya babba. Ran 27th March, 1911 suka zo Donga da zama.A zamanin Sarki Gara Garkiye II. Shi Gara Garkiye II, ya ci Sarautarsa shekara ta 1910. Amma sai a ran 28/4/1911 aka tabbatar da bikin Nadinsa. Akwai turawa uku a ranar nadinsa, wato Rev. Flemin,wakillin gwamnatin Mallaka,suka shaida nadinsa.Shi wannan Gara Garkiye II,yana da matan aurensa  guda sabain (70) chip shi kadai.Wannan mutum ne ya karbi mishanari da hanu biyu – biyu. Shine ya basu fillin gida, kusa da bakin kasuwa, kusa kuma da masallacin Garin Donga.
                A cikin watan Janairu 1913 Mr. & Mrs. Guinter daga Wukari suka kawo wata Missionary Miss. Stella Abiah Ryan a nan Donga domin bishara, ta rasu anan Donga ran 22/11/1918 kabarinta na nan Donga.
                A cikin shekara ta 1914, Rev. Whiteman ya gina dakin adada mai ciki biyu cikin station na Donga.
KARIN WASU MAISHINARI
A cikin watan janairu ta shekara 1913, Mis S.A Ryan tai so Donga domin aikin Bishara. Mr & Mrs Guinter daga Wukari suka kawo ta cikin gidan mission na Donga.Locachin da Whiteman zai tafi hutu a can Ingila, Mr.William ne ya zo ya karbi aikinsa a Donga. A cikin shekara ta 1920, Johannan Veenstra ta zo nan Nigeria.Aka tura ta zuwa Donga. Rev.Whiteman ne ya karbe ta zuwa gidan mission ta koya Hausa a Donga nan tsawun shekara daya. Daga cikin shekara 1921 ne ta tafi Lupwe,Takum. Itace mutum na farko daga CRC,SUM, America. Ta yi shekara 13 anan kasarmu. A cikin shekarar ta 1933, ran 9 ga watan Aprailu ta rasu a Asibitin VOM kusa da Jos, Jihar Plateau State.
SAMUN SABOBIN TUBA:
                Da Rev. Whiteman ya fara aikin wa’azin Bishara a nan Donga, sai Ubangiji ya bude zuciyar Habu Kunlomiya Likita da Afu, sun tuba ga barin zunubansu. A watan Janairu ta shekara 1912 ne suka shaida Yesu Almasihu a fili, suka kuma karbe shi ya zama mai Cetonsu da Ubangijinsu. Laiya Mama, ta tuba bayansu.
                A cikin shekara ta 1912 aka kara samun cigaba da masu tuba a kowane lokaci. Ran 6/8/1916, Sambo dan Gara Sonyonga wadda da shi Musulmi ne ya fita a sarari ya tuba, ya karbi Yesu Almasihu, domin ya zama Ubangijinsa da Mai Cetonsa. Da tubansa kawai, bai bata lokaci ba, ya soma wa’azin bishara ga mutanensa baji ba gain.
YIN BABTISMA TA FARKO:
                Wanda aka fara yi masa Babtisma ta farko wani mutum mai suna Istifanus Lar, wadda Mission suka zo da shi daga wase. A shekara ta 1911 ne aka yi masa Babtisma. Babtisma ta biyu a ran 2/1/1913 mutum hudu (4) dukansu yan Donga ne, wadda yayi Babtisma shine Rev. Whiteman. Rev. Guinter ne yayi waazi.Wadanda akayi masu Babtismar sune:-
                Timon mamma, Jonathan Habu, da Danyela Afu. Kuma aka ci jibin Jibin Ubangiji  Yesu a ranan.Duka masu cin Jibi suka kai mutum tara (9) yan kasa da turawa hudu(4). Wanchan Jibi na farko kennan a cikin garin Donga. Mutane suka ci gaba da tuba, ana kuma yi masu baptisma, har aka bude makaranta a janairu 1914. Wannan makaranta ta koyon karatu da rubutu ce. Yara dayawa suka iya karatu da rubutu a cikinta.
BUDE WUKARI BIBLE SCHOOL
A cikin shekara ta 1915, ran 5 ga watan Janairu aka bude Bible school na wukari, da dalibai guda 13. Hudu (4) daga cikinsu yan Donga Sune; Afu, Longha, Timon Mamma da Habu. Kudin makaranta duka naira goma ne (10:00) a shekara. Mishinari ne ke biyan kudin makarantansu. Shekaru biyu ne zaa yi a makarantar.
Da aiki ya yi wa mishinari fararen fata yawa,sai suka tsayyar da shawara cewa, a dauki dalibai wadanda suka riga suka yi shekara guda a wukari Bible School a aike su zuwa sabbobin wurare domin akin bishara. Daga cikinsu akwai yayan Donga da aka tura su zuwa wurare kamar ; Buma da matarsa aka aika zuwa Sai. Timon mamman da matarsa Hauwa zuwa Takum, shine mai bishara na farko a kasar Takum duka.Mallam Longha da matarsa Rahila zuwa Rafin Kada.Wannan a cikin shekara ta 1916 ne aka yi su. Bayan da Timon yayi shekara guda a Takum, sai Habu Likita ya je ya Karbe shi. Shi kuma ya koma Makaranta a wukari cikin 1917, Janairu.Daga baya ne Mr.Filibus Ashu, wikari,ya je ya hada kai da  Habu Likita a Takum. Ashu da Habu suna aikin tare a Takum, sai bukata ta tashi da karfi a Ibi. Wannan ya sa Habu ya koma da aikin bishara da maganinn a Ibi. Ashu kuma ya ci gaba da aikin bishara a kasar Takum.
 GINA MASUJADA (MAJAMI’A) A DONGA:
                Lokacin da Mr. Guinter da Maxwell suka zo Donga domin wa’azin Bishara ta farko tare das su akwai Rev.  Paul Burnhurt ,wadda  bamu ambaci sunansa can da fari ba.Shi Rev. Pual Brunnhurt ne ya fara kafa Bukka domin sujada ran Lahadi da wassu ranakun Addu’a a shekara ta 1908.Daga baya cikin shekara ta 1928, Mr, Maxwell da Mr. Tullock suka gina sabon majamia cikin Donga. Wannan ya fin a da girma.
KAFA EKKESIYAR GU A DONGA:
                Godiya ga Ubangiji Sarkin Ekklesiya, mai fada da cikawa ran 17/7/1917 wani abu baba ya faru a cikin Tarihin Donga, aka kafa Ekklesiyar Yesu Kristi a nan Donga a Kalkashin Sudan United Mission, (SUM).Wadanda suka kasance a wurin domin gani da idonsu wato Turawan Mishanari sune:- Rev. Guinter daga Wukari, sai shi Rev. C. L. Whiteman da Matarsa da wasu kuma.Daga cikin yan kasa da aka kafa Ekklesiya dasu, duka duka mutum goma sha (12) ne.Maza Shida (6) mata shidda ne. Daga cikin matan,biyu yayan Donga ne. Hudu kuma daga gidan yantattun bayi na Rumasha can Nasarawa state. Su biyu din kuma aka yi masu baptisma ran 17 Yuni,1917,da rana. Sune:-
          (a) Timon Mamman da Matarsa Hawa
(b)                 Jonathan da matarsa Rahilu
(c)                 Habu K. Likita da Matarsa Hawa
(d)                 Danyela Afu da Matarsa Esther
(e)                 Irimiya da Matarsa Martha
(f)                  Gadu da Matarsa Maryamu
Wadan nan yan Ekklesiya Rev. Guinter ya taddasu tsaye, yayi masu tambayoyi na karban hakin tafiyadda Ekklesiyar Kristi tsakanin dimbin matsafa, suka amsa da cewa I, zasu iya aikin da ikon Ubangiji Sarkin Ekklesiya. Daga cikinsu aka zabi Dattibai (2) biyu Dikononi biyu (2) Sa’an nan aka karanta masu Dokoki da kaida na Mulkin Ekklesiya, su kuma suka amince zasu iya daukawa daga karshe kuma suka sa hanunsu na tabbatarwa. Amma aikinsu na wata shida ne.Za a zabi shugabanni na shekara ta 1918, a watan janairu.
Banda yan ikklisiya da aka kafa ikklisiya das u, akwai mutane 20 mata da maza wadanda suka riga sun yi shaida, suna cikin classes na gabanin baptisma. Su wadannan suka kasance cikin sujada tare. Bayan hidimar kafa ikklisiyar Gu, aka ci jibin Ubangiji Yesu Kristi a ranar. Wannan hidimar jibi da yamma ne aka yi ta bayan an yi wa mata biyu baptisma. Mutane dayawa suka taru, Gara da dukan jamaarsa, wato majalisa, suka kasance cikin majamia safe da yamma. Massallata da Matsafa suka kewaye majamia domin gano wa idanunsu abin tarihi. Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah saboda yaduwar ekklisiya. Wannan abu ya faru shekaru da yawa da suka wuce.
BUDE GIDAN MISSION A LUPWE
Locachin da mallam Timmon Mamma , Mallam Habu Likita, Mallam Irimiya, Mallam Siman Attajiri da Mallam Filibus Ashu ke gogormiya da aikin yaduwar bishara, a duwatsun kasar Takum da kewaye, mission suka gan bukata babba, su bude wata tungan bishara a can kasar Takum. Saboda haka aka bude gidan mission a Lupwe, kusa da garin Takum, cikin shekara ta 1921 wadda ya zama mai gida a can itace Johanna  veenstra daga Donga.Rev. Whiteman ya raka ta.
SUDAN UNITED MISSION
Christian Reformed Church of America ta dauki aikin daga hannun British branch.(Reshen Ingilan)
Da zaman Veenstra a can, ya jawo CRC branch ta shigo nan don aikin bishara a kasarmu. Saboda haka, a cikin taron synod a shekara 1934, majalisa ta zartas da doka cewa ztat aiki mishinari zuwa nan kasarmu. A tura mishinari zuwa nan. Amma aikin kasar wukari da Donga na hannun su rahen Ingilan tukunnan sai cikin shekara ta 1940 CRC-SUM suka karbi aikin. Shekaran ne kuma aka nada Mallam Istifanus Audu a matsayin pastor na farko a CRCN.
KAFA EKKLISIYAR KRISTI A SUDAN,LARDIN BENUE.
A cikin shekara ta 1951,shugaban ikklisiya wadda ya hada da pastoci,dattawa masu bishara da mishinari suka yi taron majalisa ta farko a Ibi.A cikin wannan taro ne aka kikkiro da sunnan Eklisiya cewa “EKAS LARDIN BENUE”.An sake yin wata majalisa a watan nuwamba na 1951, a wukari. A wannan taro aka kafa kwammitin rubuta kaidodin ekklisiya. Kwammitin y agama aikinsa.
Majalisa EKAS Benue ta yi taro ran 7/Yuli/ 1954  a nan Donga. Cikin wannan taron, majalisa ta zartas da cewa wannan Eklisiya zaa rika kiranta “EKAS LARDIN BENUE”.
Bayanda aka amince da aikin kwammitin kaidodi,da kuma sunan Ekklisiya,sai aka tsayadda shawara cewa zaayi bukin kafawar Ekklisiya ran 8/8/1954 a Donga, inda aka fara kafa Ekklisiyar Gut a farko a cikin Lardin Benue. Haka aka yi.Suka zo Donga .Masu hidima sune; Rev.Smith,Mr Jonathan Wamada,Mallam Henry Bello, Rev.Pecker da Pastor Damina Bawando. Hidima da aka yi a ranar sujada da karanta tsarin dokoki wato “Constitution” ga dukan Pastoci,Dattabai masu bishara da mishinari day an tambayoyi da amsoshi ga shugabannin Ekklisiya. Yin aduoi na kafuwar Ekklisiya,jin wa’azi daga bakin Rev.Smith. Daga karshe kuma aka ci jibin Ubangiji Yesu Krisiti tare.An rufe bukin da sujadar yamma. Wadda Pastor Damina Bawando ne yayi wa’azi. Yana cewa “ Krista, ku tsaya kan Almasihu, kuma kasa kunne gareshi kullum kullum”. Yadda aka kafa Ekklisiyar Lardi a nan Donga kenan.

GINA SABON MAJAMI’A:
    Mun riga mun ambata a bisa cewa Rev. Paul Burnhut ne ya fara kafa masujada wato Bukka a Donga cikin shekara ta 1908. Amma daga can cikin shekara 1928, Mr. Maxwell da Mr. Tullock suka gina sabon Majami’a cikin garin Donga. An cigaba da amfani da wannan ginin da akayi kusa da kasuwan Donga shekara da shekaru. Sai a cikin zamanin Mallam Dawuda kwancha da ya zo a Donga a shekara ta 1930, lokacin da yake Shugabantar wannan Ekklesiya, ganin yadda mutane ke karuwa yau da gobe, sai shi da Majalisar Gu Donga suka shawarta a gina sabon Majarmi’a mai girma a cikin garin Donga. Sai aka tuntubi mai Girma Gara Donga (Marigayi) Mallam Sambo Garbosa II, nan da nan ya amince da rokonsu, ya kuma basu wannan filli wadda a ciki aka gina Majami’a da Primary School, da makabarta. An fara aiki a shekara ta 1951 an  karasa a 1952 da jinkan Ciyawa. Gannin yadda zamani ke kunno kai,sai majalisa ta zartas da cewa a kware ciyawa, a mayar da rufin da kwano. Haka aka yi a shekara ta 1965-1966.Dawuda kwancha kuma ya rasu aran 17/9/1959.
MAIKATA YAN KASA
Locachinda turawa suka kaura daga nan Donga zuwa Gindiri da Lupwe Takum,saboda rashin cigaba da koma baya cikin ayuka da kuma dalilin tsoro,aikin bishara ta koma baya sosai.Wukari ma wadda aka kafa Ekklisiyar Gu nata a shekara ta 1921 ta koma da baya.Gannain yadda Donga da Wukari suka koma baya,sai mishin da shugabannin ekklisiya na locachin suka hada wukari da Donga wuri guda a kalkashin churh na Donga. Aka rada masa suna Emmanuel Donga. Wannan ya auku a cikin shekara ta 1930. Bayan shekaru 20, wukari da Donga suka sake parpado da karfi. Gannin yadda suke murmuweya gaba gaba, sai aka sake mayar wa wukari da iznin zamanta na Gu, a cikin shekara ta 1951.Aka kuma danka Ibi, wukari,Donga kalkashin Rev.Deker.

TARIHIN MARIGAYI BABA DAWUDA KWANCHA ZUWA GA

HAIFUWA DA ASALINSA:
                Bamu san daidai shekara da aka haifi shi Mallam Dauda Kwancha ba. Amma shekarunsa ya nuna cewa an haife shi tsakannin 1886-1890 can kasar Bambur kasar wurkum,Karim Lamido Local Government,Taraba State. a cikin shekara 1886, ya karbi addinin Krista a wurin Turawan Mission ne cikin 1918, A wannan lokacin dai Baba Kwancha yana tareda Turawan Mission a Ibi nan a Ibi Local Government. A nan Inda ya koyi aikin Kafinta han yak ware ya sama gwanin Kafinta. A wannan lokaci ne ya auri farkon Uwargidansa suka Haifi diyarsu ta farko mai suna Mallama Rautha. Ita Rautha diyansa ta auri Marigayi Mai-Martaba Sarkin Wukari Mallam Abe Ali. Watau har wa yau ita Rautha tana da rai.
ZUWAR BABA DAWUDA KWANCHA DONGA:
                A lokacin da Mission suka kaura daga nan Donga zuwa can Lupwe da Gindiri cikin Shekara ta 1921, sai aikin lura da Ekkilisiya za ta koma baya sai Mallam Habu Likita wanda suke tare a can Ibi tare da Baba Kwancha ya roki Mission da su kawo aba Kwancha nan Donga, saboda cin gaban aikin Bishara. Da wanann roko ta karbu cikin shekara ta 1990, Mission suka turo Baba Kwancha a Donga inda ya ci gaba da rike kuma yada Bishara a Donga har 1959. Yana nan yana kuma cikin kafintarsa.
                A na Donga ne ita Uwargidan Baba Dawuda Kwancha na farko ta rasu. Daga nan ne ya auri Gimbiya Zainabu diyar Gara Garbosa I Mallam Sonyonga wadda aka yi mata Baptisma a shekara ta 1932 da sunan Rifkatu Dawuda Kwancha tare da ita suka Haifi Mallama Liatu wadda ta auri Marigayi (Rev) Musa Ciroma tsohon Shugaba CRCN GU I Takum.
                Baba Dawuda Kwancha dai ya yi ayyuka sosai a Donga. Ekkilisiyar Donga ta kasaita kwarai a dalilin Shugabancinsa, na takaice dai Baba Dawuda Kwancha ya rasu ya bar duniya a shekara 1959 a ranar 17th September, 1959. A wanan lokaci ne Ekkilisiya Gu Donga ta sami Pastor dan kasa watau Rev. Bulus Adi Inashi wanda ya ci gaba da lura da Ekkilesiyar Donga zuwa rasuwarsa shi ma. Haka nan a bin farin ciki yau ga mu a hade cike da godiya ga Ubangiji  Allah da murnar cikar sheharu (80) Tamanin ta kafuwar CRCN watau ginin Addinin Krista wanda duniya duk ta yi shaida cewa, Ya- ‘ yan Dawuda Kwancha Masubin Addinin Krista sun bazu tare da cin gaba a kasar Donga da Majami’u dabam cikin CRCN a garin Donga da keawayenta.
3. HIKIMAN BABA DAWUDA KWANCHA A DONGA:
1. Baban Manomi ne kwarai ga abinci a hade da dabbobi
2. Makiyayi ne na Jama’a
3. Horaren dan kasa Allah ya halliche shi da Hikima iri-iri tare ba Basira.
Cikin Rayuwan Baba Dawuda Kwancha a Donga shi ya fara kawo wadanan ga Jama’a
(a)     Injin Shinkafa
(b)      Injin saka zanuwa
(c)      Injin yin wanke-wanke
(d)      Motan Hawa (Vehicle)
(e)      Radio
(f)      Katin Kayayaki
(g)      Post Office (Postal Agency)
(h)     Truck na Dauka Kaya
A taikace dai yawancin ‘Ya’ yan gaban Baba Dawuda Kwancha nana nan ransu Miasli:-
(a)           Mai-Martaba Gara Donga na ya Viz:-
Mallam Danjuma Stephen Banyonga JP, FCIA (HON) Garbosa III.
(b)                 DR. Bitrus Gani Ikilama Babban Likita ne na kashi a Earia (A.B.U.).
Marigayi Reuben Yahaya Garpiya Ex-Member a gidan sha-warwarin Abuja watau (House of Representative) 

                                                                        
                REV. BULUS ADI INASHI

                HAIFUWA DA ASALI: Bincike ya nuna cewa an haifi Mallam Bulus Adi Inashi cikin garin Suntai nan cikin karamin hukuma ta Donga. Asalinsa kuma Bajibe ne bias ga kabila.  Iyayensa dai da matsafa ne sawu da kafa. Mallam Yariman Atiku ya zo dashi nan Donga. Inda yayi bishara har ya tuba ya karbi Yesu Almasihu ya zama mai cetonsa. Ya kuma sami baptisma ran 2/4/1950 ta hannun Rev. J. Pema, wani baturen mission.

KARATU: Mallam Bulus Adi Inashi, ya shiga Bible School a Lupwe cikin shekara ta 1947-1953. Ya gama karatunsa shekara shida. Ya shiga makarantan aikin Pastor cikin shekara ta 1954-1958, y agama.

AURE: Mallam Bulus Adi Inashi yayi aure da Gimbiya Nyungbeya a cikin shekara ta 1942. Tare da ita suka haifi yara goma (10) Takwas suna da rai, biyu ne suka rigamu zuwa hannun daman a Yesu Kristi. Domin shigan aikin Bishara yadda ya kamata, sai ita Gimbiya Nyungbeya tayi Baptisma cikin shekara ta 1950. Ran 2/4/1950 ta hannun Pastor J. Pema sunan Baptisma nata – Deborah ce. Wato rana daya ce suka yi Baptisma da mijinta.

AIKIN PASTOR: Bayan da Baba Dawuda Kwancha ya rasu cikin shekara 1959 shekaran din ne Bulus Adi Inashi ya kamala karatunsa na cikin Pastor a can Lupwe Takum, ta hannun Rev. E. Smith. Nan da nan Dattawan gu Donga suka bashi kira Bulus Adi Inashi ya kama aiki a nan Donga cikin shekara ta 1958, ya cigaba da aiki shekara ta 1978 shekaru ishirin (20) chip-chip yana shugabanta CRCN Donga. Ya kuma rasu ran 9/2/1978.

AYUKA DA BULUS INASHI YAYI: Akwai manyan manyan ayuka dayawa bayan Allah nan yayi a nan Donga. Wadanda bamu iya ambatansu ba, saboda karacin lokaci. Kima daga cikinsu sune: - Gina Primary School, Fadada Majamiu, da bude Makarantu a Kauyuka, kamar Akate, Tunari, Sanso, Suntai, Jatau, Maigoge, Mallam Yonro, Gankwe da sauransu. Bulus Adi Inashi shine ya kafa Gu na Suntai ran 7/5/1961. Ya kuma kafa Gu a Maigoge cikin shekara ta 1964. Shi Bulus Adi Inashi ne, ya kware dayawa a bisa wannan majamia, ya kuma yi rufinta da kwano cikin shekara ta 1966. A cikin zamaninsa ne Ekklesiya ta gina gidan Pastor na farko. Har yanzu shi Bulus Adi Inashi ne, ya fadada wannan majamia. A lokacin da shi Bulus Adi Inashi ke aiki anan Donga, yayi wa masu bi maza da mata da yara kanana Baptisma fiye da mutum dubu biyu (2, 000). Ayukan da Bulus Adi Inashi yayi a cikin CRCN Donga da kewaye dayawa. Mutum ne mai tsawun jimrewa da wahala saboda Bishara. Ga kuma hakuri da naciya. Ya gama aikinsa ran 9/2/178. Allah, ka bamu ruhun Rev. Bulus Adi Insahi Amen.

 REV. EZEKIEL MADAKI NUNGALA
HAIFUWA DA ASALI:
An haifi Mallam Ezekiel Madaki ciki shekara ta 1942, a nan garin Donga, shi Bachambe ne bisa ga asalinsa na kabila. Ya karbi addinin Krista har aka yi masa Baptisma ran 4/9/1960 ta hannun Rev. Bulus Adi Inashi. Yayi makarantu da dama har ya kai ga matsayin mai babban Degree na biyu (Masters Degree in Theology) ya kuma aure da Sisiliya cikin shekara ta 1972. Yanzu haka suna da yara bakwai tare. Maza biyu, mata biyar. Wannan bawan Allah ya sami cikaken goyon baya daga wurin jama’a Krista ta kasar Donga baki daya. Hard a wadanda ke ba Krista ba, suka goyi bayan shugabancinsa anan Donga. Kai cikin dukan fadin CRCN, babu wani Pastor day a sami yarda da goyon bayan Jama’a irin ta Rev. Ezekiel Nugala. Shi rev. Ezekiel Madaki Nugala ya karbi shugabancin Ekklesiyar Gu Donga ran 21/1/1979 ranan kenan aka nada shi Pastor na CRCN Donga. Yayi aiki na tsawon shekaru 15 anan. Ya bar aiki da Gu Donga ran 16/10/1994. Lokacin da yake aiki aiki anan ya ja wannan Ekklesiya zuwa gaba kwarai. Ga kima daga cikin yawan abubuwan da shi ya gudanar:- Ya kewaye gidan Ekklesiya, da masaukin baki da office na Pastor da ganuwa. Ya sayi babban injin na wuta, Ya gina clinic na CRCN a nan Donga. Ya samu manyan filaye domin Ekklesiya. Ya zama sanadin kawo Veenstra Seminary a nan Donga. Yayiwa majamia kwaskwarima domin ta dace da zamani. Ya sayi motoci biyu domin aiki cikin Ekklesiya anan Donga. Ya gina majamiu a kauyukan Denden, Sanso, Ananum da Pyewola.
                Sauranayukan da Ezekiel yayi sun hada da kafa wasu Gu, Gu kamar haka:- Tunari 17/2/1985, Akate 14/4/1985 da kuma Kapye ran 2/8/1991. Ya bude wadansu dakin sujada a kauyuka Nwonkwai, Nafada, da Weltibi.
                Banda shugabanci Gu Donga, Ezekiel ya zama shugaban Gunduman Donga, Lardin Donga, Mataimakin Babban Sakatare na CRCN, Madadin President na CRCN. Ya rike matsayi dabam-dabam cikin CRCN. Da yake Ubangiji bai nufa aikinsa ya kare cikin CRCN ba, sai ya bar aiki da Donga ran 16/10/1994. Mun gode masa kwarai.

                                                                                  
REV. YAKUBU NUMSHI MASOYI
                HAIFUWA DA ASALI: An haifi Pastor Y. Masoyi ran 30/9/1948, a kauyen Vingam, Bogoro LGA Bauchi State. Shi Basayi ne bisaga asalinsa na kabila. Lokacin da aka haifeshi, iyayensa matsafa ne, domin Yakubu Numshi Masoyi, ya tuba ya karbi addinin Krista a shekara ta 1964, watan Octoba na shekaran din. A cikin shekara ta 1968, ran 7/7/1968, ya sami Baptisma ta Rev. Habila Adda Angyu, na Wukari. Yayi aure da Zainab Haruna ran 4 Janairu 1976. Cikin shekara din ne. Ita Zainab ta sami Baptisma ta hannun Rev. Bulus Inashi a nan Donga ran 17/7/1976 da suna Saratu. Yenzu haka suna da yara 8 tare, maza hudu mata ma hudu. Shirin Allah kenan.
ZUWANSA NAN DONGA: Kafin Pastor Yakubu Numshi Masoyi yayi aiki a wurare dabam-dabam ya fara aikin Pastor da CRCN Gu Nyakwala cikin shekara ta 1981-1985 ran 8/2/1981 ne aka nada shi Pastor na CRCN. Bayan shekaru biyar a Nyakwala ya tafi CRCN Yola, can Yola yayi shekaru tara (9) lokacin ya fadada CRCN zuwa Jalingo, Wuroboki da Mubi. Cikin shekara ta 1994 ya dawo da aikin cikin CLTC Wukari. Bayanda Rev. Ezekiel Nugala ya bar nan ran 16/10/1994. Majalisar CRCN Donga ta wurin izinin RCC Donga da kuma GCC na CRCN ta kira Pastor Masoyi a cikin shekara ta 1995. Ran 1/4/1995 Rev. Yakubu Numshi Masoyi ya zo nan Donga. Majalisa babban ta tabbatar da shi Pastor na CRCN Donga ran 8/4/1995.
                Ko da shike Pastor bai zauna a bakin aikinsa sosai ba, saboda makaranta wadda ya koma yi cikin wata na tara (9) 1995. Duk da haka mun ga kamun ludayinsa ko. Idan har mai iko duka ya barmu da rai tare da Rev. Masoyi, to babu shakka zata kai ga samun ruwa a nan Donga. Da zuwansa kawai ya kafa Gu a Sanso ran 3/6/1995, ya kara masu Bishara a kauyuka guda biyu (2) wato Irimiya Gani da Bulus S. Ibrahim tare da Yohanna Azetu, yanzuu haka CRCN Donga tana bishara guda uku (3) bana an bude CRCN Church a hanyin Gundu. Majamia ta Pyewola kuma an jinkata bara. Har bara an gina dakin Sunday School na yara mai class hudu (4) manya manya. Kai hart a bikin nan da muke ciki, shine ya tsiro da tunanin yin haka. Muna addu’a da fatan cewa Allah ya bamu lafiya tare Amin.
REV. THEOPHILUS ZANDO


REV. WISDOM SURUPE




REV. ZACHARIAH DANGANA AGBAKYENI

HAIHUWA
An haifi Rev.Zachariah Agbakyeni a cikin shekara 1956 wa iyalin marigayi Mallam Akinda Agbakyeni Abite da Mallama Amonye Agbakyeni cikin garin Ibi, a Ibi Local Government Area, Taraba State.

TUBA
Rev.Agbakyeni ya ji maganar Yesu Almasihu a bakin wayansu yan’uwarsa  masunta a locachin da suke kama kifi a  Lake Chad. Dagan an ne ya karbi yesu Almasihu ya zama Mai Cetonsa. Aka kuma yi masa baptisma da dawowarsa a gida cikin garin Ibi.
MAKARANTA
Rev. Zacharia ya fara makarantar Firamari a Ekas Primary School, daga shekara 1977 zuwa 1981 a cikin garin Ibi. Bayan ya kamala makarantar Firamari, ya  kuma sami shiga cikin makarantar Smith  Bible College,Baissa a jihar Taraba, inda ya kamala wannan karatun a cikin shekara 1983. Y a shiga Gindiri College of Theology daga 1988 zuwa 1992 inda ya sami takardar Diploma in Theology. Daga nan Rev.Agbakyeni ya shiga TCNN Bukuru daga 1999 zuwa 2001. Nan ne ya sami  Bachelor Degree in Divinity.
AURE
Rev.Zachariah Agbakyeni ya Auri matarsa Esther Magaji a cikin shekara 1984. Suna jiran Ubangiji ya Albarkace su da yaya.
AIKI
Rev.Agbakyeni yana da kwarewa a fannoni dabandaban. Ya fara aikin Mai Bishara a cikin garin Ibi a shekara 1983 zuwa 1988 a cikin CRCN Church Gu Ibi. Sai aka yi masa transfer  zuwa CRCN Jos inda ya zama Pastor na farko a wannan Ekklisiyar daga 1996 zuwa 1999. Daga baya, komiti na transfer suka yi masa transfer daga CRCN,Jos zuwa CRCN  Rafin Kada,inda yayi aiki daga 199 zuwa 2004. Cikin shekara  2004 aka yi masa transfer zuwa CRCN Tsokundi inda yayi aiki daga 2004 zuwa 2007. Daga cikin garin Tsokundi aka yi wa Rev. Zachariah Agbakyeni transfer zuwa CRCN Head Quarters inda ya yi aiki na Assistant General Secretary na CRCN daga 2007 zuwa 2011. Dagan an ne aka yi masa transfer  zuwa CRCN Gu Donga inda yake aikin Pastor yanzu.
AYUKANDA  REV AGBAKYENI  YAYI
A cikin zaminsa na Pastor a Ibi ne aka gina da jinkan CRCN Nyonyo da ke cikin garin Ibi a yanzu. A cikin Jos kuma, a locachinsa ne aka sayi filinda da aka gina CRCN Jos a yanzu. Har yanzu, a locachinsa ne aka sayi kayan kidi na zamani, wato musical Instrument a CRCN Jos.
Cikin Rafinkada kuma,  a locachinsa ne aka gina masujada da ake sujada a cikin yanzu amma bai iya jinka ba  har aka yi masa transfer. A locachinsa ne aka kuma sayi Musical Instruments a cikin CRCN Rafin Kada aka kuma gina guest House a cikin idan Ekklisiya da wasu ayuka.
A Tsokundi, Ubangiji ya bashi ikon gina Katanga kewaye da masujada na CRCN,Tsokundi tare da kuma Dattabansa  da kuma sayan musical instruments.
A cikin garin Donga, Ubangiji ya fara amfani da shi a fannoni daban daban. Makrantar Ekklisiyar CRCN Donga  ta kuma koma a permanent side. A locachinsa ne aka gyara CRCN Gu Donga yadda yake a yanzu da kuma sayan Benches da wasu kayan kide kide na zamani.
MUKAMMAI  DA YA KAMA
Rev. Agbakyeni ya fara aikin Deacon a CRCN Ibi, yayi aikin Dattijo da kuma Secretary a CRCN Gu Ibi, ya kuma yi akin mai bishara a maternity da clinic na Ibi.
Yayi aikin secretary na Gundumar Ibi na tsawon shekaru shida (6), Assistant Secretary RCC Ibi shekaru Uku (3), Assistant Treasurer RCC Wukari na Shekaru Uku (3),Chairman, Gundumar Rafin Kada na shekaru Uku, Vice Chairman, RCC Nyankwala daga 2001 zuwa 2003,Chaiman RCC Nyankwala 2003 zuwa 2007, Assistant General Secretary CRCN 2007 zuwa 2o11.
Yanzu Rev Zachariah yana rike da mukamin Pastor CRCN Gu Donga da kuma Chairman, CRCN Pastors.


WADANSU MANYA SHAMKA DA MUKE DA SU
1.       Sabon Majamia.
 Wannan daki da muke ciki a yau an gina tun 1951, anyi masa gyaran fuska cikin 1966, yanzu haka ya kasa mana. Saboda haka mun yi shiri mu gina sabon gidan sujada wadda zata dauki mutane 2500 lokacin sujada guda. Kwamiti sun Kiyasta cewa zamu kasha kudi N 50,000,000.00 (Miliyan Hamsin)
2.       Nursery and Primary School:
Mun shirya don mu bude Nursery da Primary School anan. Har ma mun kusa kamala gina azuzuwa. Idan Allah, ya yarda mana, Kuma kwamiti sun yi aikinsu haikan, to zamu bude wadannan makarantu a watan satumba 1997.
3.       Gina Recreation,
Ganin yadda mutane ke shan wahala da neman wurin shakatawa lokatan bukukuwan aure, taron dukan masu bi, taron kungiyin siyasa, taron kungiyoyi Jama’a  da sauran taruruka na inganta rayuwa Jama’a kasa da addini. Mun dauka tamkar haki ne a wuyanmu. Saboda haka mun shirya domin mu gina recreational centre. Inda za a tanada zauren taro (conference Hall) masaukin baki, falin wassanin motsa Jiki, Filin silma da video, dakin na domin hira a waje, da saurane   kayayaki masu kawaita rayuwa ta ruhuniya da nay au da kullum.
4.  Fadada aikin Bishara.
     Mun shirya mu fadada yaduwar Bishara zuwa; Katsina Ala can Benue State, Lafiya, Nasarawa state, Bauchi, Bauchi State da wassu sabobin wurare. Wadannre duka zamu yi su ta wurin aikadda masu bishara.
5   .  Mota da Generator.
Mun yi niyya mu tada wadannan kayan aiki wadda a halin yanzu hakam, sun jin gine sabida rashin kudi. Idan Allah ya bude mana hanya to zamu tadasu. Saboda muna bukata kudi kimanin dubu dari da tasain (N 190.000.) kafin mu tada su.
6   . Heaith clinic.
CRCN Rural health program sun riga sun daga daraja primary Health Clinic namu zuwa Comprehensive Health Clinic tare da maternity. Wannan sashe kuma muna bukata kimanin kudi naira Dubu dari uku da hamsin (N350,000.00) kafin komai ya tafi daidai bisa ga dokokin Hukuman kiwon Lafiya. Muna rokonku ku tayamu da addu’a domin cimma wadannan sharuka.


                                         KIRA GA:-
CRCN Headquarters da mission nata. Tun da mission sun tashi nan cikin kasa, a shekara ta 1921. Babu wani mission day a zauna a nan Donga, sai cikin shekara ta 1990 danuwa Mr. Bob Lodewyk ya zo ya bude Veensttra Seminary a Donga. Da yake Veensta Seminary kadara na CRCN da missionary muna roko cewa wadanda abin ya shafa, da su daukaka makaranta. Su bude primary a wurin, su inganta makaranta mata, su hada makaranta da wani jamia domin bada diploma da degree, su bude Day Secondary School, su fadada gidajen ma’aikata da kuma dakunan Dalibai, su bude part time courses domin pastoci masu aiki, su gina babban dakin karatu (Library) su bude Clinic domin makaranta da kuma sayan mota saboda makaranta.
 Ya’yan Donga.
Muna kira ga ‘ya’yanmu na Donga da masu kauna da Ekklesiya, da su bamu gudumawarsu, na kudi, ko shawara, ko kaya da kuma addu’a, saboda mu samu cin nasarar kamala sharukan mud a muka ambata a bisa.
Donga Local Government.
Muna kira ga Chairman na Donga Local Government Area, Mallam Salihu Waziri Mamman day a bamu goyon baya da taimakon kudin do min aikin recreation centre da comprehensive Health Centre.




4 comments:

  1. MAY THE ALMIGHTY GOD BLESS ALL OUR FORMER PASTORS ARE THEIR FAMILY.

    ReplyDelete
  2. SUCH A BEAUTIFUL STORY AND HISTORY

    ReplyDelete
  3. MAY THE ALMIGHTY GOD BLESS ALL OUR FORMER PASTORS ARE THEIR FAMILY (KUBUZA ISHAKU)

    ReplyDelete